*DAREN LAILATUL KADARI* *Yazo a cikin Hadisi, ana samun Daren Lailatul* *Kadari a kwanakin goman na karshen watan Ramadan a daren ashirin da Daya(21) ko ashirin da Uku(23) ko ashirin da* *Biyar(25) ko ashirin da Bakwai(27) ko ashirin da Tara (29) daren na karshen watan Ramadan.* *Nana Aisha (R.A) tace,* *Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Ku nemi Daren Lailatul Kadari a goman karshe.” (Bukhari ne ya rawaito).* *Ana so a yawaita addu’a a Daren Lailatul Kadari. Nana Aisha (R.A) ta ce, na tambayi Manzon Allah (S.A.W)a ce, ya Rasulullahi, idan na ga Daren Lailatul Kadari me zan fada a cikinsa? Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, ki ce:* "اللَّهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّى." *“Allahumma innaka afuwun tuhibbul afwa fa’afu anni.”* *Ma’ana: “Ya Ubangiji, hakika, Kai mai afuwa ne, kuma kana kaunar yin afuwa, ya Allah ka yi min afuwa.” (Bukhari da* *Muslim ne suka rawaito).* *Kuma ana so a karanta wadannan ayoyi masu yawan lada.* 1- آيَةُ الْكُرْسِيُّ 2- آمَنَ ا...