Za a kasa kudaden marigayi Abacha tsakanin kasashe uku Najeriya da Amurka da tsibirin Jersey sun ce za su kasafta fiye da dala milyan 267 da tsibirin Jersey ya kwace daga irin kudaden da ake zargin gwamnatin tsohon shugaban Najeriya na soja, marigayi janar Sani Abacha ta sata ta jibge a bankunan kasar. A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai aka sanya dala 267 a cikin wani asusu na musamman da gwamnatin kasar ta Jersey ta kafa domin zuba irin wadannan kudade masu kama da ganima. Wani wakili daga ofishin ministan shari'ar kasar ya shaida wa BBC cewa har kawo yanzu Jersey ba ta kammala tantance hanyar da za ta bi ba wajen kasafta kudaden ba. Sai dai ya ce gwamnatin tsibirin za ta zauna da Najeriya da Amurka domin tattauna yadda za su raba kudin a tsakaninsu. Gwamnatin Najeriya za ta rabawa talakawa kudaden Abacha 'Kudin da Abacha ya sace': Switzerland za ta mayar wa Nigeria $320m A baya dai wata kotu a Amurka ta gano kudaden wadanda ta ce an fitar da su daga Najeriya ta wasu ...