Za a kasa kudaden marigayi Abacha tsakanin kasashe uku
Najeriya da Amurka da tsibirin Jersey sun ce za su kasafta fiye da dala milyan 267 da tsibirin Jersey ya kwace daga irin kudaden da ake zargin gwamnatin tsohon shugaban Najeriya na soja, marigayi janar Sani Abacha ta sata ta jibge a bankunan kasar.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai aka sanya dala 267 a cikin wani asusu na musamman da gwamnatin kasar ta Jersey ta kafa domin zuba irin wadannan kudade masu kama da ganima.
Wani wakili daga ofishin ministan shari'ar kasar ya shaida wa BBC cewa har kawo yanzu Jersey ba ta kammala tantance hanyar da za ta bi ba wajen kasafta kudaden ba.
Sai dai ya ce gwamnatin tsibirin za ta zauna da Najeriya da Amurka domin tattauna yadda za su raba kudin a tsakaninsu.
Gwamnatin Najeriya za ta rabawa talakawa kudaden Abacha
'Kudin da Abacha ya sace': Switzerland za ta mayar wa Nigeria $320m
A baya dai wata kotu a Amurka ta gano kudaden wadanda ta ce an fitar da su daga Najeriya ta wasu bankunan Amurkar, kafin daga bisani a karkatar da akalarsu zuwa tsibirin na Jersey.
An dai zargi marigayi janar Sani Abacha da wawure dukiyar kasa inda aka fitar da ita zuwa kasashe daban-daban.
To sai dai rahotanni a wasu kafafan watsa labaran Najeriya da Burtaniya sun rawaito cewa Burtaniya ta karbe kudin daga wani banki a tsibirin na Jersey.www.facebook.com/ibrahim sani hussainwww.bbchausa.com
AREWASTARBLOG: Video: Kalli Yadda Ake Hada Connection Na Yadda Z... : Video: Kalli Yadda Ake Hada Connection Na Yadda Zaka Saurari Duk Kanin Kiran Da BUDURWARKA Takeyi Ko Akai Mata Ta Wayar Ka " SPY...
Comments