Skip to main content

Posts

Showing posts with the label SHUGABA
Shugaban Tunisia Beji Caid Essebsi ya rasu Fadar shugaban kasar Tunisia ta sanar da mutuwar shugabanta Beji Caid Essebsi, wanda ya mutu yana da shekara 92. Shi ne shugaban kasar da ya fi kowa tsufa a duniya. An kwantar da shi a asibiti ranar Laraba amma jami'ai ba fadi dalilin rashin lafiyar tasa ba. A shekerar 2014 ne Mista Essebsi ya lashe zaben farko na kasa tun bayan boren kasashen Larabawa. Mista Essebsi ya kuma kwanta a asibiti a watan da ya gabata bayan fama da abin da jami'ai suka kira "rashin lafiya mai tsanani." Ba su yi karin bayani kan batun ba. Firai Minista Youssef Chahed, wanda ya ziyarce shi a asibiti, ya roki mutane da su daina yada "labaran karya" a kan halin da shugaban ke ciki. A tsarin kundin tsarin mulkin kasar, Mista Chahed zai iya zama shugaban kasa na tsawon kwanakin da ba za su wuce 60 ba ko kuma zuwa lokacin da za a zabi sabon shugaba. A farkon shekarar nan ne ya sanar da cewa ba zai tsaya a zaben da za a sake yi a watan Nuwamba ba...