Skip to main content
Shugaban Tunisia Beji Caid Essebsi ya rasu Fadar shugaban kasar Tunisia ta sanar da mutuwar shugabanta Beji Caid Essebsi, wanda ya mutu yana da shekara 92. Shi ne shugaban kasar da ya fi kowa tsufa a duniya. An kwantar da shi a asibiti ranar Laraba amma jami'ai ba fadi dalilin rashin lafiyar tasa ba. A shekerar 2014 ne Mista Essebsi ya lashe zaben farko na kasa tun bayan boren kasashen Larabawa. Mista Essebsi ya kuma kwanta a asibiti a watan da ya gabata bayan fama da abin da jami'ai suka kira "rashin lafiya mai tsanani." Ba su yi karin bayani kan batun ba. Firai Minista Youssef Chahed, wanda ya ziyarce shi a asibiti, ya roki mutane da su daina yada "labaran karya" a kan halin da shugaban ke ciki. A tsarin kundin tsarin mulkin kasar, Mista Chahed zai iya zama shugaban kasa na tsawon kwanakin da ba za su wuce 60 ba ko kuma zuwa lokacin da za a zabi sabon shugaba. A farkon shekarar nan ne ya sanar da cewa ba zai tsaya a zaben da za a sake yi a watan Nuwamba ba. A wani taro ya shaida wa jam'iyyarsa ta Nidaa Tounes cewa ya kamata wani mai jini a jika ya karbi ragamar. Ya ce lokaci ya yi da "za a bai wa matasa dama." Mista Essebsi tsohon lauya ne da ya yi karatu a birnin Paris na Faransa. A lokacin da yake dan siyasa na tsawon lokaci ya kuma yi ministan harkokin cikin gida da kuma kakakin majalisar wakilai. A shekarar 2011 ne aka hambarar da tsohon shugaban Tunisiya Zine el-Abedine Ben bayan shafe shekara 23 a kan mulki. Tun sannan ake jinjinawa Tunisiya kasancewarta kasar da ita kadai ta hau turbar dimokradiyya bayan boren kasashen Larabawa. Sai dai a shekarun baya-bayan nan kasar ta sha fama da hare-haren masu ikirarin jihadi da kuma tabarbarewar tattalin arziki, inda yawan marasa aikin yi ke ta'azzara. Labarai masu alaka Tunisiya Tura wannan labarin Game da aika wa Koma sama Kewaye a shafin BBC Copyright © 2019 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka. AFP

adamusuleimanbasawa@gmail.com

Comments

Popular posts from this blog

MAN YAN HANYOYI 10 NA YIN ARZIKI

MANYAN HANYOYI GUDA GOMA-(10) NA SAMUN ARZIKI Arziqi yana da manyan hanyoyin samunsa guda biyu sune; *A-Hanyar samu🎆n Arziqi na Al'ada Wanda ya hada noma da kiyo da kasuwanci da kwadago*. *B-Hanyar samun arziqi na shari'a,sune wadan nan hanyoyi guda goma,wadanda suka tabbata daga Alqurani da Hadisan Manzon AllahSAW ingantattu* Dukkan Wanda yake neman Arziqi to wajibine ya bi daya ko wasu daga cikin wadan nan hanyoyi tare da doguwa ga Allah,sannan ya kuma yarda da abinda Allah ya bashi na kason arziqinsa. Daga Cikin ayoyin da suke bayani a akan arziqi da hanyar samun sun hada da;- ﻳﻘﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ;(ﻭَﻓِﻲ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀِ ﺭِﺯْﻗُﻜُﻢْ ﻭَﻣَﺎ ﺗُﻮﻋَﺪُﻭﻥَ‏) . *(Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari)*. @ﺳﻮﺭﺓ:ﺍﻟﺬﺍﺭﻳﺎﺕ. ﻭﻳﻘﻮﻝﺗﻌﺎﻟﻰ (ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻫُﻮَ ﺍﻟﺮَّﺯَّﺍﻕُ ﺫُﻭ ﺍﻟْﻘُﻮَّﺓِ ﺍﻟْﻤَﺘِﻴﻦُ ‏) . *(Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi)*. @ﺳﻮﺭﺓ : ﺍﻟﺬﺍﺭﻳﺎﺕ ﻭﻳﻘﻮﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ ‏(ﻫُﻮَ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺟَﻌَﻞَ ﻟَﻜُﻢُ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽَ ﺫَﻟُﻮﻟًﺎ ﻓَﺎﻣْﺸُﻮﺍ...