Skip to main content

Posts

Showing posts with the label *Yadda Ake Yin Sallar Jana'iza

*Yadda Ake Yin Sallar Jana'iza

*Yadda Ake Yin Sallar Jana'iza * 'YAN-UWA mafi yawancinmu, muna yin Sallar Jana'iza amma kuma ba mu san abinda ake fada a cikin kowacce Kabbara ba. Dan haka ya sa muka ga cewa yana da kyau mu ware wani lokaci na musamman, Domin fahimtar da mu yadda ake yin sallar Jana'za. 'YAN-UWA ita dai Sallar janai'za, tana da babban lada, ga wanda ya aikata ta kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar, dan haka yana da kyau, mu tsaya mu koya. Kamar yadda na ce, sallar jana'za tana da kabbarori guda hudu ne kawai kuma kowacce Kabbara da abin da ake fada a cikinta. 1. KABBARA TA FARKO ana karanta {suraul-fatiha} ne kawai, banda wata sura, ko wata a'ya. 2. KABBARA TA BIYU ana karanta Salatin Annabi ba wani salati na daban ba. 3. KABBARA TA UKU ana yin addu'a ga wanda ya mutu mace ko namiji. 4. KABBARA TA HUDU za ka yi addu'a ne ga sauran al'ummar Musulmi Wadanda suke  Raye da matattu. DAN UWA KANA GAMAWA sai ka jira Liman ya yi sallama.