Skip to main content

Posts

Showing posts with the label DUNIYA MAKARANTA

DUNIYA MAKARANTA

*DUNIYA MAKARANTA * "Ma'aunin gane mai arziki shine a duba ni'imar da yake da ita wanda kudi basu samar da ita." *Dr. Mansur Sokoto .* * DUNIYA MAKARANTA * "Idan rayuwar ka tana cikin jin dadi, zaka rika ganin komai kyakykyawa ne a idonka. Idan kana da koshin zuci kadan zai wadace ka. Idan ka yarda da Allah komai sai yazo maka cikin sauki." *Dr. Mansur Sokoto.* * DUNIYA MAKARANTA * "Abu biyu ne suke daga darajar dan Adam: Amfanin jama'a da hakurin cutarwar su. Abu biyu kuwa suna tunkude musiba: sadaka da sada zumunci." *Dr. Mansur Sokoto.* *DUNIYA MAKARANTA * "Idan ka fadawa mutum gaskiya, kamar ka shayar dashi kofin madaci ne. Bai kamata kayi tsammanin ya gode maka ba." * Dr. Mansur Sokoto.* *DUNIYA MAKARANTA * "Duniya abun hawar ka ce, idan ka tuka ta sai ta kaika inda kake so. Amma idan ta tuka ka to zata kai ka mahallaka." *Dr. Mansur Sokoto* *DUNIYA MAKARANTA* "Duk yadda ibada tayi tsanani wah...