MENENE MA A CIKI TUKUN?. Zan danyi magana ne akan wani abu danaga yana yawan faruwa da yan uwa mata da maza, sau da yawa inna fahimci hakan ko naga wani yana magana da korafi, sai tunani ya fara ciyartar zuciyata. Menene ke haifar da akasarin lalacewar soyayya tsakanin mata da maza? Sai karamin tunani irin ta kwakwalwata yakaini ga wata matsaya, matsayar kuwa itace; Son Shahara. Ko wacce Mace yanzu burinta shine tazama ta sami saurayi ko ince mijin da zata aura yazama shahararre, Shara a kudi, ilimi, ko Wani Babban aiki ko uwa ubama abin da suka fi so shine ace mutum yana karatu a Kasar waje. Wannan yayi tasiri gaya a zukatan mutane, basu duba zuciyar mutum da kuma hadafinsa kan tafiyar addini, sau tari abinda kake tunanin mutum, sai kaga daga baya ka fahimci ba haka yake ba, me yasa?. Saboda ka biyo wani abu ne da kake ganin yana dashi, dazarar ka fahimci hakikaninsa saikai tunanin canza reshen da kake kai, wannan yasa soyayyar yan uwanmu mata da maza bata kai labari mafi...