Skip to main content
MENENE MA A CIKI TUKUN?.

Zan danyi magana ne akan wani abu danaga yana yawan faruwa da yan uwa mata da maza, sau da yawa inna fahimci hakan ko naga wani yana magana da korafi, sai tunani ya fara ciyartar zuciyata.

Menene ke haifar da akasarin lalacewar soyayya tsakanin mata da maza? Sai karamin tunani irin ta kwakwalwata yakaini ga wata matsaya, matsayar kuwa itace; Son Shahara.

Ko wacce Mace yanzu burinta shine tazama ta sami saurayi ko ince mijin da zata aura yazama shahararre, Shara a kudi, ilimi, ko Wani Babban aiki ko uwa ubama abin da suka fi so shine ace mutum yana karatu a Kasar waje.

Wannan yayi tasiri gaya a zukatan mutane, basu duba zuciyar mutum da kuma hadafinsa kan tafiyar addini, sau tari abinda kake tunanin mutum, sai kaga daga baya ka fahimci ba haka yake ba, me yasa?.

Saboda ka biyo wani abu ne da kake ganin yana dashi, dazarar ka fahimci hakikaninsa saikai tunanin canza reshen da kake kai, wannan yasa soyayyar yan uwanmu mata da maza bata kai labari mafi yawan lokuta.

Wani zakaga yana da budurwa amma yana sonta ne don yaga kamar tana da wani abu dazarar ya zauna ya karanceta sarai saisu zama sun "BreakUp" me yasa?.

Dama wannan abinda take dashi ya biyo, kuma ya gane babu shi, hakama mata, yakamata mu zauna muyi wa kanmu karatun ta natsu, mu so juna don Allah, mu gina soyayyar kan tafarkin Allah tare da neman zabin alkhairi dake ciki.

Wannan shiya fi dacewa damu, ba neman shahara ko suna a cikin kawaye ko abokai ba, kai burinka a ce kaine saurayin wance mai kaza da kaza ko yar gidan wane.

Ke kuma kawaye suyita famfa ki kina sahan kamshi ala dole kina soyayya da mai karatu a kasar waje ko wani sanannen mutum ko mai kudi.

Mecece ribar da za'a girba a wannan ginin tubalin tokar da zai iya gushewa wata rana? Addini baibar komi ba saida ya warware  mana shi, ka nema sanin yadda ake fara neman masoyi da yadda zaka sami masoyi na gari mai riko da addini.

Domin da yawan lokuta wajen da kake tunanin samun farin ciki da walwalar da zata baka damar yin ibada cikin tsafta, sai kaga baka samu ba, ya kamata mu hankalta.

Ina rokon Allah mai girma da buwaya Ni da Ku ya datar da mu ga hanya mafi dacewa tafarkin tsira da amincewar Allahu swt domin babu abinda ke bayansu sai dacewa da gidan Al-jannatul firdous.

(Khayri the daughter of islaam).

Comments

elbasawee.com said…
Allah yasaka da alkhairi

Popular posts from this blog

Kungiyar IZALA tayi Allah wadai da cin Mutunci da yan kwankwasiyya suka yiwa Dr. Ali Pantami

Kungiyar IZALA tayi Allah wadai da cin Mutunci da yan kwankwasiyya suka yiwa Dr. Ali Pantami Daga Ibrahim Baba Suleiman Kungiyar wa'azin musulunci ta Izalatil Bid'ah wa Iqamatis Sunnah a Naijeriya, Tayi Allah wadai da cin Mutuncin da 'yan kungiyar kwankwasiyya sukayi wa ministan sadarwan Naijeriya Sheikh Dr. Isa Ali Pantami a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano dake Birnin kano. Shugaban IZALA Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau, shi yayi wannan kira ta wayar tarho daga Birnin Maiduguri jihar Borno a tarayyar Naijeriya, inda yake halartar wani taro a Birnin na Shehu. Sheikh Bala Lau yace, wannan al'amari akwai damuwa kwarai cikinsa, Malami mahaddacin Al'qur'ani, masanin tafsiri, Wanda ya kare rayuwarsa wajen aiki da fadakarwa akan addinin Musulunci, shine wasu 'yan Siyasa zasu masa irin wannan cin Mutunci tabbas an aikata laifi Babba. Shehin Malamin yayi kira da babbar murya cewa jagoran kwankwasiyya Dr. Rabi'u Musa kwankwaso ya fito ya baiwa ya...

SABON HANYAR TARA KUDI TA HANYAR SPIN-SPIN.

SABON HANYAR TARA KUDI TA HANYAR SPIN-SPIN.  Assalamu alaikum. yakai mai sauraro wannan wata damane dazaka samu kuɗi ta kamfanin Globalwealth batare dashan wani wahalaba, Domin nasan dayawanmu munkasance masujin tsoron kwashemana kuɗi babu gaira babu dalili, to wannan yasha banban ,Domin shi wannan ba talla bane shi spin-spin ne kawai zakayi kullum sau 6 arana.  YAYA AKE TARA KUƊI DASHI.  => An biya ku don kashe lokaci akan shafin ta hanyar zubi da keken hannu - kullun kuna samun ramuka 6 don buga spin-spin kuma zaku iya yin tsakanin #300 - #600 kowace rana daga , to kaga kenan misali idan kana samun #300 kullum #300*30= #9000. Idan kuma kanayin #600*30 = #18000 Wannan kuɗin kana iya samune kawai idan bakai Referral koɗaya ba, idan kuma kana da Referral kaga kenan zai iya wucewa. https://www.globalwealthz.com.ng/signup?ref=ibrahim072  => Kuna samun damar zuwa kayan kayan aji na farko waɗanda zasu kashe muku kuɗi mai yawa kyauta  => A...