Skip to main content

Posts

Showing posts with the label LABARIN 'YAN SHI'A

Labarin 'yan shi'a

Labari da dumi duminsa    'Yan Shi'a sun dakatar da zanga-zanga, sun bayyana dalilansu Kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) ta aka fi sani da Shi'a ta sanar da cewa za ta dakatar da zanga-zangar da ta keyi na dan wani lokaci. Shugaban fanin yada labarai na kungiyar ta IMN, Ibrahim Musa ne ya sanar da hakan cikin wata jawabi da ya fitar a ranar Laraba. Gwamnatin Tarayya ta ayyana kungiyar a matsayin na ta'addanci tare da haramta ayyukan kungiyar bayan kotun tarayya da ke Abuja ya ayyana kungiyar a matsayin na ta'addanci. Musa ya ce an dauki matakin dakatar da zanga-zangar ne sakamakon 'wasu sabbin hanyoyi da suke bude na warware matsalar' da ke da alaka da haramta ayyukan kungiyar. Ya ce kungiyar ta dauki matakin dakatar da zanga-zangar ne saboda girmama wasu manyan mutane da suka saka baki kan batun . Ya kara da cewa idan har aka samu wasu suna zanga-zanga a wani sashi na kasar, hakan ka iya faruwa ne idan wasu ba su fahimci sakonsa ba ko kuma sharri ...