Skip to main content

Labarin 'yan shi'a

Labari da dumi duminsa
   'Yan Shi'a sun dakatar da zanga-zanga, sun bayyana dalilansu Kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) ta aka fi sani da Shi'a ta sanar da cewa za ta dakatar da zanga-zangar da ta keyi na dan wani lokaci. Shugaban fanin yada labarai na kungiyar ta IMN, Ibrahim Musa ne ya sanar da hakan cikin wata jawabi da ya fitar a ranar Laraba. Gwamnatin Tarayya ta ayyana kungiyar a matsayin na ta'addanci tare da haramta ayyukan kungiyar bayan kotun tarayya da ke Abuja ya ayyana kungiyar a matsayin na ta'addanci. Musa ya ce an dauki matakin dakatar da zanga-zangar ne sakamakon 'wasu sabbin hanyoyi da suke bude na warware matsalar' da ke da alaka da haramta ayyukan kungiyar. Ya ce kungiyar ta dauki matakin dakatar da zanga-zangar ne saboda girmama wasu manyan mutane da suka saka baki kan batun . Ya kara da cewa idan har aka samu wasu suna zanga-zanga a wani sashi na kasar, hakan ka iya faruwa ne idan wasu ba su fahimci sakonsa ba ko kuma sharri ce kawai da jami'an tsaro ke niyyar yi musu domin bata musu suna. Ga wani sashi na sanarwar "Kungiyar Islamic Movement in Nigeria tana sanar da 'yan Najeriya da kasashen waje cewa ta dakatar da zanga-zangar ta na neman sakin El-Zakzaky a titunan Najeriya saboda wasu sabbin cigaba da aka samu dangane da karar da lauyoyin mu suka shigar kan haramta ayyukan mu da gwamnatin tarayya tayi a wannan makon. "Kungiyar ta dauki wannan matakin ne saboda girmama wasu manyan mutane da kungiyoyi da suke neman ganin an warware matsalolin da ke faruwa kuma nuna fatan za a samu masala kuma a saki shugaban mu da aka tsare kusan kimananin shekaru hudu." Me za kuce akan hakan?

Comments

Popular posts from this blog

MAN YAN HANYOYI 10 NA YIN ARZIKI

MANYAN HANYOYI GUDA GOMA-(10) NA SAMUN ARZIKI Arziqi yana da manyan hanyoyin samunsa guda biyu sune; *A-Hanyar samu🎆n Arziqi na Al'ada Wanda ya hada noma da kiyo da kasuwanci da kwadago*. *B-Hanyar samun arziqi na shari'a,sune wadan nan hanyoyi guda goma,wadanda suka tabbata daga Alqurani da Hadisan Manzon AllahSAW ingantattu* Dukkan Wanda yake neman Arziqi to wajibine ya bi daya ko wasu daga cikin wadan nan hanyoyi tare da doguwa ga Allah,sannan ya kuma yarda da abinda Allah ya bashi na kason arziqinsa. Daga Cikin ayoyin da suke bayani a akan arziqi da hanyar samun sun hada da;- ﻳﻘﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ;(ﻭَﻓِﻲ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀِ ﺭِﺯْﻗُﻜُﻢْ ﻭَﻣَﺎ ﺗُﻮﻋَﺪُﻭﻥَ‏) . *(Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari)*. @ﺳﻮﺭﺓ:ﺍﻟﺬﺍﺭﻳﺎﺕ. ﻭﻳﻘﻮﻝﺗﻌﺎﻟﻰ (ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻫُﻮَ ﺍﻟﺮَّﺯَّﺍﻕُ ﺫُﻭ ﺍﻟْﻘُﻮَّﺓِ ﺍﻟْﻤَﺘِﻴﻦُ ‏) . *(Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi)*. @ﺳﻮﺭﺓ : ﺍﻟﺬﺍﺭﻳﺎﺕ ﻭﻳﻘﻮﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ ‏(ﻫُﻮَ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺟَﻌَﻞَ ﻟَﻜُﻢُ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽَ ﺫَﻟُﻮﻟًﺎ ﻓَﺎﻣْﺸُﻮﺍ...