DAKIN LABAREN HAUSA
23 sep 2019
KARKEN ALEWA KASA, BATURE GAGARE Page 1 Episode 1
KARKEN ALEWA KASA, BATURE GAGARE
Daga littafin Karshen Alewa Kasa
Na Bature Gagare
(c) NNPC Nigeria
BABI NA FARKO
TSAUNIN GWANO Tin kwal, Tin kwal, kwal!
Tin kwal, Tin kwal Kwal…
Mai yin shela ya bar kada kugensa
domin ya yi
jawabi a wani dan lungu da ya shigo.
Ya kafa hannu a baki yayi kira, “Hyai, hyai,
ina mazajen
Tsaunin Gwano, sarkin kira ya
gaishe ku. Bayan
gaisuwa ya ce a fada muku lokaci ya
yi wanda duk mai ji da kanshi ya shirya…”
Ya wuce gaba yana kada kuge yana
fadar sako
rariya rariya. Hantsi ya ajiye kokon
da ya gama
shan burkutu da shi, ya yi wata doguwar mika ya
yi murmushi, “To fa mutane, ga
Audun makeri
can yana buga kugen tasa. Yaya ka
ji Mailoma?”
Wani saurayi da ake kira Mailoma yana zaune a
kan wani buzu da aka yi da fatar biri
ya miko
hannu suka tafa, ”Haba Hantsi,” in ji
shi, “Ai ni
nan wurin duk sun tsima ni kuma, sai na ji ma
giyar nan duk ta fita raina.” Sai wuf
ya mike
tsaye gaban Hantsi yana gyaran
lagen gwadonsa.
Yace, “Bara kuwa an yi farauta da sa’a. Ka tuna
lokacin da muka darkaki katuwar
barewar nan?
Wuu, an yi tsiya ranar nan ka ji.”
Hantsi ya kara ciko kokonsa da giya
ya ce, “A wannan rana ai duk tsawon raina ba
zan iya
mantawa da ita ba. Ko ba ranar da
kuka goge
raini ba da Dano dan sarkin Arna?
Lallai da ban sa baki ba ai da kun yi danyen aiki,
ya miko
masa giya cikin koko, Mailoma ya
karba ya ce,
“Ai da ranar nan sai na kas shi
aradu.” Sai ya daga hannuwa sama yana kirari shi
daya.
Can sai ya duka ya dauko wani goran
giya wanda
suka shanye yace, “Amshi nan
Hantsi ka buga mini takena in dan fara yi kafin gobe
da safe ta
yi.” Hantsi ya goge bakinsa ya yi
dariya ya gyara
zama, “To matsa can baya idan
rawa zaka yi. Kada ka yi mana asarar giya, na ga
kana
tangadi.” Sai ya sami wani dan iccen
ya fara
kida da gora, shi kuma Mailoma ya
koma bari daya yana takawa yana kirarin da ya
saba yi:
Ni ne na bara ni ne na bana,
Kuma ni ne na shekarar basasa.
Ni ne na Hantsi ba mamaki,
Mijin Tayani dogon yaro. Samun irin ku sai an tona.
Yaro ko kana musu in ci ubansa.
Dano ya buga damu ya kasa…
Sai ya ci gaba da rawa yana tsalle
tsalle. Hantsi
kuwa yana tsugune yana barka dariya, “To bari
mu sake kida yanzu,” in ji shi. “Bari in
buga
maka “Aci lugui-lugui” ka taka.” Da
ya sake kida,
sai Mailoma ya dafe kansa askakke da hannu
daya, ya daga gudan a sama ya yi
ruri,
“Wayyahu! ….. Ihuuu!!”
Wani tsoho wanda yake zaune yana
jemar fata ya firgita ya kwatsa musu tsawa,
“Yaya haka?
Wadanne irin yara ne haka marasa
ladabi. Don
sakarcin banza sai a rasa wajen ihu
sai cikin gida.” Suka bar abin da suke yi suka
juyo wajen
shi suna harara wai don ya katse
musu jin dadi.
Tsohon nan ya dubi Mailoma ya ce,
“Kai kuma ina zuwa gonar ka debo ma jakai
kara, hala ma
ya sha ruwa?”
Mailoma ya dan sunne kai yana
murmushi, “A’a
Baba, niyyata in tashi mu tafi ni da Tayani idan
giyar nan ta kare.”
Dan tsohonnan ya ce, “Zancen
banza, ga shi har
maraice zai yi ka shantake?”
Shi Wannan dan tsohon sunansa Chiwake. Duk
garin Tsaunin Gwano da kewaye an
san shi da
yin jima. Wannan sana’a da yake yi
ta sa a
kullum ba ya rasa abin yin kayan miya. Mailoma
da Hantsi duk ‘ya’yansa ne, kuma su
kadai ne
gareshi. Su kuma yaran ‘yan biyu ne,
kuma a
halin yanzu karfinsu ya kawo sosai. Mailoma
shekarunsa sha bakwai. Yana da
tsawo
gwargwadon shekarunsa. Yaro ne
mai hali da
kyau, kuma ga rashin tsoro. Tun yana dan
shekara shida Chiwake yake tafiya
da shi wajen
farauta. Sukan yi kamar wata guda a
Jeji suna
farauta ba su shigo gari ba, amma Mailoma ko
kuka ba ya yi musu ya ce yana son
zuwa gida.
STOP POINT
A gaban shi sai mazaje su bi naman
jeji a guje su
kama su yanka. Wani lokaci ma ka ga an
harkume da fada wajen rabon nama
ana buge
buge da yanke-yanken juna. Tun
yana tsoron irin
wadannan miyagun abubuwan har ya zo yana
sha’awarsu.
Hantsi kuwa natsatsen yaro ne
wanda ba ya son
yawan fitinu. Duk yawanci idan za a
je farauta shi ya fi son ya tsaya gida ya yi jima
a
maimakon ya je yawon banza a jeji.
Shi yasa
wani lokaci sai samari su rika
kiransa na-mata. “Tayani,” Mailoma ya yi kira. “Tayani
ina kika
shige ne?”
Wata murya daga can wajen da ake
daure
dabbobi ta ce, “Haba ga ni nan zuwa. Ina jika
igiyoyi ne.”
Mailoma ya yi kira da karfi, “to yi
maza ki kare
mana. Ga Baba nan za ya cinye ni
danye.” Mahaifiyarsu Mailoma ta baro
tukunyar miya da
tsumangiya a hannu ta nufo Mailoma
a fusace.
Shi kuma kafin ta iso wurin shi sai ya
fita waje da gudu. Sauran mutanen gida suka
yi ta dariya.
Tayani ta fito waje da igiya a hannu
domin su
tafi gona. Sai dariya take yi ma
mijinta saboda koro shi da aka yi. Wannan yarinya
Allah ya ba ta
wani abu wai shi kyau. Cikakkiyar
budurwa ce,
wadda yanzu shekarunta daya da
rabi da auren Mailoma. Ita ba a yi mata irin
tsagarsu ta
Maguzawa ba, shi ya sanya kyawon
nata ya kara
fitowa sosai da sosai. Bayan haka
ga kuma kirar jiki wajen Tayani kamar su goga da
Amina
sarauniyar Zazzau. Ba ta da yawan
magana
kamar mijinta, amma duk lokacin da
ta yi sai mutum yaji kamar mawakiya don
zakin murya. A
takaice ma dai duka mutanen gari su
a
tsammaninsu wannan yaron ya yi
mata asiri ne har ta yarda ta aure shi. Ita ce
wadda cikin masu
neman auren ta har da su Dano dan
Sarkin Arna.
Amma duk a wofi; ta tsaya a kan
Mailoma sai an aura mata shi har iyayen ta suka gaji
suka
amince.
“To mu tafi gonar ko mu dawo da
wuri,” Tayani
ta ce. Mailoma ya dube ta ya ce, “Tayani
bana son kina
zuwa gona kullum. Yanzu duk za ki
lalace jikinki
ya zama irin na Marka kishiryar
Inna.” Tayani ta yi murmushi irin wanda
yake sare ma
mazaje zukatansu, ta dube shi da
idanunta masu
kamar auduga ta ce, “Dubi jikina.”
Yaro ya karbi hannun da ta miko masa yana
shafawa. Tayani
fara ce kamar bafillatana. Ta ce,
“Shekara guda
ke nan ina zuwa daji tare da kai,
amma ban sake wata kama ba, yanda ka sanni a da
haka nake
yanzu. Ko kuwa yau giyar ta fada
maka karya
ne?”
at 07:45
Share
No comments:
Post a Comment
Links to this post
Create a Link
‹
›
Home
View web version
Powered by Blogger.
AREWASTARBLOG: Video: Kalli Yadda Ake Hada Connection Na Yadda Z... : Video: Kalli Yadda Ake Hada Connection Na Yadda Zaka Saurari Duk Kanin Kiran Da BUDURWARKA Takeyi Ko Akai Mata Ta Wayar Ka " SPY...
Comments