Allah ya yiwa tsohon kwamishinan Kaduna, Abdulsalam Baba Ahmed rasuwa Updated: 10 hours ago Author: ibrahim sani hussain Views: 2335 Category: Labarai FACEBOOK EMAIL TWITTER WHATSAPP FACEBOOK MESSENGER TELEGRAM - Tsohon kwamishinan filaye na jihar Kaduna, Abdulsalam Baba Ahmed ya rasu, a ranar Talata, 4 ga watan Yuni bayan yayi fama da rashin lafiya - Babban dan Marigayin, Hakeem Baba Ahmed ne ya tabbatar da rasuwar mahaifin nasa ga manema labarai - Anyi jana'izarsa a gidan ahlin Baba Ahmed da ke Tudun Wada, Zaria a yau Talata Allah ya yiwa tsohon kwamishinan filaye na jihar Kaduna, Abdulsalam Baba Ahmed rasuwa, a ranar Talata, 4 ga watan Yuni bayan yayi fama da rashin lafiya. Marigayin ya rasu yana da shekaru 53 a duniya. Babban dansa, Hakeem Baba Ahmed ne ya sanar da hakan ga manema labarai a garin Zaria. Ya bayyana cewa mahaifin nasa ya rasu da misalin karfe 3:00 na rana a Kaduna. Kafin a nada shi a matsayin kwamishina a gwamnatin Ramalan Yero, marigayin yayi aiki a matsayin shu...