GWMANAN JAHAR KADUNA MALNASIRU AHMAD EL-RUFA'I YACE CIKIN ALƘAWURA 18 BIYARNE 5 BAI SAMU DAMAR CIKAWABA
Cikin Alkawurra 81 Da Na Dauka A Lokacin Yakin Neman Zabe, Biyar Ne Ban Samu Damar Cikawa Ba, Cewar Gwamna El-Rufai Na Kaduna Daga Comr Abba Sani Pantami Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa tun a farkon kamfen din sa ya dauki wasu alkawurra har 81. A wadannan alkawurra kuwa gwamna El-Rufai ya ce duk ya cika da dama, wasu kuma ana aikin cika su. Wannan da wasu batutuwan duk na kunshe ne a wani rahoton BBC wanda ta wallafa a shafinta bayan taron tattaunawa na ke-ke da ke-ke da gwamnan jihar Kaduna, inda al’ummar jihar suka samu damar yi masa tambayoyi kan alkawuran da ya dauka lokacin yakin neman zabe da kuma lokacin karbar mulki. Gwamna El-Rufai ya ce wasu guda biyar ne suka gagare shi iya cikawa har zuwa yanzu. “Da muka fara neman shugabancin wannan jihar mun y i alkawura guda 81, kuma lokacin da za a sake wannan zaben na baya mun duba mun ga wane alkawarin ne muka cika, wanne ne muke kan cikawa, kuma wanne ne ba mu cika ba. “Cikin alkawurra 81, biyar ne kawai wadand...