GWMANAN JAHAR KADUNA MALNASIRU AHMAD EL-RUFA'I YACE CIKIN ALƘAWURA 18 BIYARNE 5 BAI SAMU DAMAR CIKAWABA
Cikin Alkawurra 81 Da Na Dauka A Lokacin Yakin Neman Zabe, Biyar Ne Ban Samu Damar Cikawa Ba, Cewar Gwamna El-Rufai Na Kaduna
Daga Comr Abba Sani Pantami
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa tun a farkon kamfen din sa ya dauki wasu alkawurra har 81.
A wadannan alkawurra kuwa gwamna El-Rufai ya ce duk ya cika da dama, wasu kuma ana aikin cika su.
Wannan da wasu batutuwan duk na kunshe ne a wani rahoton BBC wanda ta wallafa a shafinta bayan taron tattaunawa na ke-ke da ke-ke da gwamnan jihar Kaduna, inda al’ummar jihar suka samu damar yi masa tambayoyi kan alkawuran da ya dauka lokacin yakin neman zabe da kuma lokacin karbar mulki.
Gwamna El-Rufai ya ce wasu guda biyar ne suka gagare shi iya cikawa har zuwa yanzu.
“Da muka fara neman shugabancin wannan jihar mun y i alkawura guda 81, kuma lokacin da za a sake wannan zaben na baya mun duba mun ga wane alkawarin ne muka cika, wanne ne muke kan cikawa, kuma wanne ne ba mu cika ba.
“Cikin alkawurra 81, biyar ne kawai wadanda tunda aka zabe mu muka kasa farawa.”
A cikin alkawurran biyar da gwamnan ya ce bai cika ba akwai wasu muhimmai guda biyu da suka hada da samar da gidaje akalla 20,000 cikin shekaru hudu da gina titin jirgin kasa na zamani da zai rika jigila a cikin garin Kaduna.
Bayan haka gwamna El-Rufai ya cika wasu alkawurra da ya dauka, da wasu da ake yi zuwa yanzu da suka hada da sabonta birnin Kaduna, saka yara makarantun gwamnati kyauta, bunkasa samar da kudaden shiga da sauran su.
Wadannan ayyuka ba a cikin garin Kaduna ba kawai har da wasu manyan kananan hukumomin jihar ake yin su.
Wannan taro da BBC ta shirya, ya ba mutane damar yi wa gwamna El-Rufai tambayoyi akan wasu abubuwa da suka shige musu duhu a jihar da kuma wadanda suke neman karin bayani.
Game da kiwon lafiya kuwa, gwamna El-Rufai ya yi kira ga iyaye da su rika kai ‘ya’yan su da basu wuce shekaru biyar ba asibitin gwamnati ana duba su kyauta.
Sannan ya ce gwamnati na ci gaba da maida hankali matuka wajen inganta tsaro a fadin jihar.
Sai dai kuma duk da wannan kuri da El-Rufai yayi, mahalarta wannan taro sun musanta wasu nasarorin da ya ce an samu a karkashin gwamnatin sa.
Wasu sun koka cewa, har yanzu suna biyan kudin asibiti wa matan su da ‘ya’yan su, cewa ba gaskiya bane ake fadi wa gwamna wai kyauta ake ba marasa lafiya magani a asibitocin jihar.
Wasu mata da suka halarci taron sun shaida wa gwamna cewa lallai akwai lauje a nadi, domin hatta allura da za ayi wa ‘ya’yan su sai sun siye shi. Babu inda ake basu ko yayan su magani kyauta a asibitocin Kaduna.
BBC ta ruwaito cewa lallai fa ra’ayoyi dai sun banbanta game da ko gwamna El-Rufai ya taka rawar da ta dace wajen cika alkawurran da ya dauka ko kuma a’a.
Majiyarmu ta bi ba’asin kalaman da gwamna El-Rufai yayi a wajen wannan tattaunawa na BBC inda ta nemo ji daga wasu mazauna cikin garin Kaduna.
Wasu sun koka cewa ko gyaran cikin garin Kaduna da ake yi yanzu, ba don talakawa a ke yi ba. Domin duk inda ake gyarawa unguwanni ne na masu kudi.
” Idan ka duba gyaran da gwamna ya ke yi a Kaduna duk unguwanni ne na masu hali. Babu wani unguwa da talakawa ke da yawa da aka shiga aka yi manyan tituna ko ayyukan ci gaba.” Inji Hamza Gabaji, mazaunin Kaduna.
Sai dai kuma wasu da dama su rika saka wa gwamna El-Rufai da addu’o’in gama wa lafiya bisa ayyukan ci gaba da yake yi a jihar.
Comments