Skip to main content

Posts

Showing posts with the label PROP.IBRAHI MAKARI

MAKAFI NA KORAFI KAN BUHARI YAHASHI MINISTA

Makafi na korafi kan hana su minista a gwamnatin Buhari Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon: Sakataren kungiyar makafi ta Arewacin Najeriya Muntari Saleh ya yi Allah wadai da jerin sunayen ministocin Shugaban Kasar Muhammadu Buhari. A ranar Talata ne Shugaba Buhari ya saki jerin sunaye 43 na ministocin Najeriya. Muntari Saleh ya ce ya kamata mutane masu nakasa su samu wakilci a jerin ministocin. Ya kara da cewa nakasa ba kasawa ba ce, tun da ba ido ko hannu ne ke rike minista ba, ilimi ne, "idan neman kuri'a ne sai a neme mu amma idan dadi ya zo sai a manta da mu," a cewarsa.