Allah ya yiwa tsohon kwamishinan Kaduna, Abdulsalam Baba Ahmed rasuwa
Updated: 10 hours ago
Author: ibrahim sani hussain
Views: 2335
Category: Labarai
FACEBOOK EMAIL
TWITTER WHATSAPP
FACEBOOK MESSENGER TELEGRAM
- Tsohon kwamishinan filaye na jihar Kaduna, Abdulsalam Baba Ahmed ya rasu, a ranar Talata, 4 ga watan Yuni bayan yayi fama da rashin lafiya
- Babban dan Marigayin, Hakeem Baba Ahmed ne ya tabbatar da rasuwar mahaifin nasa ga manema labarai
- Anyi jana'izarsa a gidan ahlin Baba Ahmed da ke Tudun Wada, Zaria a yau Talata
Allah ya yiwa tsohon kwamishinan filaye na jihar Kaduna, Abdulsalam Baba Ahmed rasuwa, a ranar Talata, 4 ga watan Yuni bayan yayi fama da rashin lafiya.
Marigayin ya rasu yana da shekaru 53 a duniya.
Babban dansa, Hakeem Baba Ahmed ne ya sanar da hakan ga manema labarai a garin Zaria. Ya bayyana cewa mahaifin nasa ya rasu da misalin karfe 3:00 na rana a Kaduna.
Kafin a nada shi a matsayin kwamishina a gwamnatin Ramalan Yero, marigayin yayi aiki a matsayin shugaban karamar hukumar Zaria, sannan ya riki mukamai daban-daban a gwamnati na kungiyoyi masu zaman kansu.
Anyi sallar jana’izarsa a gidan ahlin Baba Ahmed da ke Tudun Wada, Zaria
AREWASTARBLOG: Video: Kalli Yadda Ake Hada Connection Na Yadda Z... : Video: Kalli Yadda Ake Hada Connection Na Yadda Zaka Saurari Duk Kanin Kiran Da BUDURWARKA Takeyi Ko Akai Mata Ta Wayar Ka " SPY...
Comments