*Yadda Ake Yin Sallar Jana'iza*
'YAN-UWA mafi yawancinmu, muna yin Sallar Jana'iza amma kuma ba mu san abinda ake fada a cikin kowacce Kabbara ba.
Dan haka ya sa muka ga cewa
yana da kyau mu ware wani lokaci na musamman, Domin fahimtar
da mu yadda ake yin sallar Jana'za.
'YAN-UWA ita dai Sallar janai'za, tana da babban lada, ga wanda ya aikata
ta kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar, dan haka yana da kyau, mu tsaya mu koya.
Kamar yadda na ce, sallar jana'za tana da kabbarori guda hudu ne
kawai kuma kowacce Kabbara da abin da ake fada a cikinta.
1. KABBARA TA FARKO ana karanta {suraul-fatiha} ne kawai, banda wata sura, ko wata a'ya.
2. KABBARA TA BIYU ana karanta Salatin Annabi ba wani salati na daban ba.
3. KABBARA TA UKU ana yin addu'a ga wanda ya mutu mace ko namiji.
4. KABBARA TA HUDU za ka yi addu'a ne ga sauran al'ummar Musulmi Wadanda suke Raye da matattu.
DAN UWA KANA GAMAWA sai ka jira Liman ya yi sallama.
Ita kuma sallamar guda daya ce tak! Kuma za ka yi ta ne a bangaren damanka.
Allah muke roko da ya kara tabbatar damu akan Sunnar Annabin Rahama, Manzon Allah (S.A.W).
Akwai bukatar a yada Wan nan Sako Dan Allah ta Hanyar Share. domin 'yan uwa musulmai su karu. Allah yabada ikon Hakan Ameen

Comments