Skip to main content
*DAREN LAILATUL KADARI*
*Yazo a cikin Hadisi, ana samun Daren Lailatul* *Kadari a kwanakin goman na karshen watan  Ramadan a daren ashirin da Daya(21) ko ashirin da Uku(23) ko ashirin da* *Biyar(25) ko ashirin da Bakwai(27) ko ashirin da Tara (29) daren na karshen watan Ramadan.*
*Nana Aisha (R.A) tace,* *Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Ku nemi Daren Lailatul Kadari a goman karshe.” (Bukhari ne ya rawaito).*
*Ana so a yawaita addu’a a Daren Lailatul Kadari. Nana Aisha (R.A) ta ce, na tambayi Manzon Allah (S.A.W)a ce, ya Rasulullahi, idan na ga Daren Lailatul Kadari me zan fada a cikinsa? Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, ki ce:*
"اللَّهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّى."
*“Allahumma innaka afuwun tuhibbul afwa fa’afu anni.”*
*Ma’ana: “Ya Ubangiji, hakika, Kai mai afuwa ne, kuma kana kaunar yin afuwa, ya Allah ka yi min afuwa.” (Bukhari da* *Muslim ne suka rawaito).*
*Kuma ana so a karanta wadannan ayoyi masu yawan lada.*
1- آيَةُ الْكُرْسِيُّ 2- آمَنَ الرَّسُولُ 3- إِذَا ذُلْزِلَتِ اْلأَرْضُ 4- قُلْ يَأَيُّهَا الْكَافِرُونَ 5- قُلْ هُوَ الله أَحَدٌ 6- سُورَةُ يَاسِين.


*1. Ayatal Kursiyyu*
*2. Amanar-Rasulu*
*3. Izazul zilatul ardu*
*4. Kulya ayyuhal kafiruna*
*5. Kul huwallahu ahad*
*6. Suratu Yasin.*

*Kuma a yawaita istigfari, tasbihi, salati ga Annabi, sannan a roki alhairan duniya da na lahira. Allah yasa mudace yabamu alkhairin dake cikin wannan wata Mai daraja Amin🙏🙏*
*BY JABIR AHMAD*

Comments

Popular posts from this blog

MAN YAN HANYOYI 10 NA YIN ARZIKI

MANYAN HANYOYI GUDA GOMA-(10) NA SAMUN ARZIKI Arziqi yana da manyan hanyoyin samunsa guda biyu sune; *A-Hanyar samu🎆n Arziqi na Al'ada Wanda ya hada noma da kiyo da kasuwanci da kwadago*. *B-Hanyar samun arziqi na shari'a,sune wadan nan hanyoyi guda goma,wadanda suka tabbata daga Alqurani da Hadisan Manzon AllahSAW ingantattu* Dukkan Wanda yake neman Arziqi to wajibine ya bi daya ko wasu daga cikin wadan nan hanyoyi tare da doguwa ga Allah,sannan ya kuma yarda da abinda Allah ya bashi na kason arziqinsa. Daga Cikin ayoyin da suke bayani a akan arziqi da hanyar samun sun hada da;- ﻳﻘﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ;(ﻭَﻓِﻲ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀِ ﺭِﺯْﻗُﻜُﻢْ ﻭَﻣَﺎ ﺗُﻮﻋَﺪُﻭﻥَ‏) . *(Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari)*. @ﺳﻮﺭﺓ:ﺍﻟﺬﺍﺭﻳﺎﺕ. ﻭﻳﻘﻮﻝﺗﻌﺎﻟﻰ (ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻫُﻮَ ﺍﻟﺮَّﺯَّﺍﻕُ ﺫُﻭ ﺍﻟْﻘُﻮَّﺓِ ﺍﻟْﻤَﺘِﻴﻦُ ‏) . *(Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi)*. @ﺳﻮﺭﺓ : ﺍﻟﺬﺍﺭﻳﺎﺕ ﻭﻳﻘﻮﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ ‏(ﻫُﻮَ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺟَﻌَﻞَ ﻟَﻜُﻢُ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽَ ﺫَﻟُﻮﻟًﺎ ﻓَﺎﻣْﺸُﻮﺍ...