Kungiyar IZALA tayi Allah wadai da cin Mutunci da yan kwankwasiyya suka yiwa Dr. Ali Pantami Daga Ibrahim Baba Suleiman Kungiyar wa'azin musulunci ta Izalatil Bid'ah wa Iqamatis Sunnah a Naijeriya, Tayi Allah wadai da cin Mutuncin da 'yan kungiyar kwankwasiyya sukayi wa ministan sadarwan Naijeriya Sheikh Dr. Isa Ali Pantami a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano dake Birnin kano. Shugaban IZALA Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau, shi yayi wannan kira ta wayar tarho daga Birnin Maiduguri jihar Borno a tarayyar Naijeriya, inda yake halartar wani taro a Birnin na Shehu. Sheikh Bala Lau yace, wannan al'amari akwai damuwa kwarai cikinsa, Malami mahaddacin Al'qur'ani, masanin tafsiri, Wanda ya kare rayuwarsa wajen aiki da fadakarwa akan addinin Musulunci, shine wasu 'yan Siyasa zasu masa irin wannan cin Mutunci tabbas an aikata laifi Babba. Shehin Malamin yayi kira da babbar murya cewa jagoran kwankwasiyya Dr. Rabi'u Musa kwankwaso ya fito ya baiwa ya...
Comments