Skip to main content

Labaran Yammacin Litinin 03/02/2020CE - 08/06/1441AH. Cikakkun labaran

Labaran Yammacin Litinin 03/02/2020CE - 08/06/1441AH. Cikakkun labaran

 Boko Haram sun kashe sojoji 3 sun kwace motocin yaki 2 a Borno.

 Gobara ta kama ofishin hukumar INEC a jihar Imo.

 Gwamnatin jihar Lagos ta sa an kama mashuna da Keken NAPEP fiye da 250 sakamakon sanya dokar hana achaba a jihar.

 Kotu ta yanke wa wasu 'yan fashi da makami biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya a Jos.

 Sanata Ali Ndume ya koka kan yadda al’amarin tsaro a arewa maso gabas ke kara tabarbarewa, ya yi kira ga  Buhari da ta dauki mataki.

 Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya ce lallai idan gwamnatin jihar ta cigaba da kwace filayen jama'a za su yi zanga-zanga.

 Ministan Sufuri, Amaechi ya ce gwamnati ba za ta kara farashin tikitin jirgin kasa ba na Kaduna zuwa Abuja domin a bai wa talakawa dama.

 Za a bai wa fararen hula makamai domin yaki da ta'addanci a Burkina Faso.

 Kungiyar OIC ta yi watsi da shirin shugaba Trump na Amurka na zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

 Amurka ta gayyaci shugaban kasar Sudan zuwa Washington a wata ziyara irin ta ta farko cikin shekara 30.

 Kasar Ghana za ta yi bincike kan zargin cin hanci a kamfanin jiragen sama na Airbus.

Comments

Popular posts from this blog

MAN YAN HANYOYI 10 NA YIN ARZIKI

MANYAN HANYOYI GUDA GOMA-(10) NA SAMUN ARZIKI Arziqi yana da manyan hanyoyin samunsa guda biyu sune; *A-Hanyar samu🎆n Arziqi na Al'ada Wanda ya hada noma da kiyo da kasuwanci da kwadago*. *B-Hanyar samun arziqi na shari'a,sune wadan nan hanyoyi guda goma,wadanda suka tabbata daga Alqurani da Hadisan Manzon AllahSAW ingantattu* Dukkan Wanda yake neman Arziqi to wajibine ya bi daya ko wasu daga cikin wadan nan hanyoyi tare da doguwa ga Allah,sannan ya kuma yarda da abinda Allah ya bashi na kason arziqinsa. Daga Cikin ayoyin da suke bayani a akan arziqi da hanyar samun sun hada da;- ﻳﻘﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ;(ﻭَﻓِﻲ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀِ ﺭِﺯْﻗُﻜُﻢْ ﻭَﻣَﺎ ﺗُﻮﻋَﺪُﻭﻥَ‏) . *(Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari)*. @ﺳﻮﺭﺓ:ﺍﻟﺬﺍﺭﻳﺎﺕ. ﻭﻳﻘﻮﻝﺗﻌﺎﻟﻰ (ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻫُﻮَ ﺍﻟﺮَّﺯَّﺍﻕُ ﺫُﻭ ﺍﻟْﻘُﻮَّﺓِ ﺍﻟْﻤَﺘِﻴﻦُ ‏) . *(Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi)*. @ﺳﻮﺭﺓ : ﺍﻟﺬﺍﺭﻳﺎﺕ ﻭﻳﻘﻮﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ ‏(ﻫُﻮَ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺟَﻌَﻞَ ﻟَﻜُﻢُ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽَ ﺫَﻟُﻮﻟًﺎ ﻓَﺎﻣْﺸُﻮﺍ...