Skip to main content

DOGON BURI

. Watarana Annabi Isa (A.S) YaZo Wucewa Ta Kusa Da Wani Dutse Sai Yaga Wani Dattijo Yana Ta Yin Ibada a Gefen Dutsen a Tsakar Rana, Zafi Ko Sanyi Ba Ya Damunsa. . Sai Ya Ce Masa:"Bawan ALLAH Mai Zai Hana Ka Gina Ma Kanka 'Daki Ko Rumfa Wanda Zai Kiyayeka Daga Zafi Da Sanyi, Kuma Ka Rika Yin Ibadarka a Ciki!" . Sai Mutumin Ya Ce:"Ya Ruhallahi!! Wasu Annabawa Kafin Ka Sun Bani Labarin Cewa Ba Zan Wuce Shekaru Dari Bakwai (700) a Duniya Ba. Shi Yasa Hankalina Bai Kwanta Ba, Ballantana Har In Shagaltu Da Yin Ginin Daki, Kar Ya Shagaltar Da Ni Daga Biyayyar ALLAH". . Sai Annabi Isa (A.S) Yace Masa;"A Karshen Zamani Akwai Wasu Al'ummar Da Zasu Zo, Yawancinsu Basu Wuce Shekaru 100 (Dari) a Duniya, Amma Har Zasu Rika Gina Benaye!" . Sayyiduna Aliyu (R.A) Yace;"Dogon Buri Yana Mantar Da Mutum Daga Tunanin Lahira". . To 'Yan Uwa Sai Mu Rage Burin Zaman Duniya. Mu Rika Kokarin Gyaran Gidan Lahira. . ALLAH YA BAMU WADATAR ZUCI, YA SA MU GAMA DA DUNIYA LAFIYA BIJAHI S.AW . Dan Allah idan ka karanta kayi sharing koda a group 10 ne domin yan uwa sugani su amfana• Don't forget to like

Comments