Skip to main content

GOBE SALLAH

Yanzu-yanzu: Gobe Sallah, Mai alfarma Sarkin Musulmi ya sanar Updated: 38 minutes ago Author: ibrahim sani hussain Views: 1880 Category: Labarai FACEBOOK EMAIL TWITTER WHATSAPP FACEBOOK MESSENGER TELEGRAM Labarin da muke kawo muku kai tsaye daga fadar mai alfarma sarkin Musulmi, Sultan Abubaakar Sa'ad na nuna cewa an ga sabuwar jaririyar watar Shawwal, a yau Litinin 29 ga watan Ramadan wanda yayi daidai da 3 ga watan Yuni, 2019. Sarkin Musulmi ya sanar da cewa gobe, ranar Talata ce 1 ga watan Shawwal kuma ranar Sallar Eidul Fitr. Yace: Bisa ga shari'ar Musulmi, muna masu sanar muku da cewa a yau Litinin 3 ga watan Yuni 2019 wanda yayi daidai da 29 ga watan Ramadan 1440, ne karshen watan Ramadana na shekarar 1440AH." "Mun samu rahotannin tabbacin ganin wata daga shugabannin adinin Musulunci daga gari daban-daban.. Mai martaba Shehun Borno, Sarkin Gwandu, Sarkin Jema'a, Sarkin Damaturu, da wasu sa sassan jihar sokoto Bisa da haka, gobe Talata 4 ga watan Yuni, 2019 ta zama 1 ga watan Shawwal 1440AH kuma ranar Sallah. Muna rokon Allah ya karba ibadun da mukayi a cikin watar Ramadan." Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu. Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Comments

Popular posts from this blog

MAN YAN HANYOYI 10 NA YIN ARZIKI

MANYAN HANYOYI GUDA GOMA-(10) NA SAMUN ARZIKI Arziqi yana da manyan hanyoyin samunsa guda biyu sune; *A-Hanyar samu🎆n Arziqi na Al'ada Wanda ya hada noma da kiyo da kasuwanci da kwadago*. *B-Hanyar samun arziqi na shari'a,sune wadan nan hanyoyi guda goma,wadanda suka tabbata daga Alqurani da Hadisan Manzon AllahSAW ingantattu* Dukkan Wanda yake neman Arziqi to wajibine ya bi daya ko wasu daga cikin wadan nan hanyoyi tare da doguwa ga Allah,sannan ya kuma yarda da abinda Allah ya bashi na kason arziqinsa. Daga Cikin ayoyin da suke bayani a akan arziqi da hanyar samun sun hada da;- ﻳﻘﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ;(ﻭَﻓِﻲ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀِ ﺭِﺯْﻗُﻜُﻢْ ﻭَﻣَﺎ ﺗُﻮﻋَﺪُﻭﻥَ‏) . *(Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari)*. @ﺳﻮﺭﺓ:ﺍﻟﺬﺍﺭﻳﺎﺕ. ﻭﻳﻘﻮﻝﺗﻌﺎﻟﻰ (ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻫُﻮَ ﺍﻟﺮَّﺯَّﺍﻕُ ﺫُﻭ ﺍﻟْﻘُﻮَّﺓِ ﺍﻟْﻤَﺘِﻴﻦُ ‏) . *(Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi)*. @ﺳﻮﺭﺓ : ﺍﻟﺬﺍﺭﻳﺎﺕ ﻭﻳﻘﻮﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ ‏(ﻫُﻮَ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺟَﻌَﻞَ ﻟَﻜُﻢُ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽَ ﺫَﻟُﻮﻟًﺎ ﻓَﺎﻣْﺸُﻮﺍ...