Kudirin addini: CAN da JNI sun sha ban-ban a Jihar Kaduna
Updated: 7 hours ago
Author: Muhammad Malumfashi
Views: 2300
Category: Labarai , Siyasa
FACEBOOK EMAIL
TWITTER WHATSAPP
FACEBOOK MESSENGER TELEGRAM
Kungiyoyin addini a jihar Kaduna sun nuna mabanbantan ra’ayi a game da sabuwar dokar addinin da za a kawo. A Ranar Juma’a 7 ga Watan Yuni, 2019, ne majalisar dokokin jihar ta amince da wannan kudiri.
Mista Sunny Akanni, wanda ya na cikin manyan kungiyar Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN), yayi barazanar maka majalisar dokokin jihar Kaduna a kotu, a dalilin amincewa da wannan kudiri da ya kawo surutu.
Akanni yake cewa majalisar jihar Kaduna ta sabawa umarnin kotu na rattaba hannu a kan wannan doka da zai yi wa sha’anin addini garambawul. PFN tace maganar ta na gaban kotu amma majalisa ta yi mursisi.
Haka zalika kungiyar CAN ta bayyana cewa za ta duba wannan kudiri, inda ta nuna cewa ta na da ja da wannan doka da ake shirin kawowa. Shugaban kiristocin jihar Kaduna, Joseph Hayab ya bayyana wannan.
KU KARANTA: Lashe zabe dabam da sa-hannun Sanatoci a Majalisa – Ndume
Ita kuma kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), ta yi farin ciki da jin labarin wannan doka. Yusuf Adamu, wanda shi ne Sakataren kungiyar JNI ya fito ya ce babu wata matsala tattare da wannan kudiri da aka kawo.
Yusuf Adamu yake cewa duk wanda zai yi wa’azi yadda ya dace bai kamata ya ji tsoron dokar da za a kawo ba. Kungiyar tace CAN ba ta bada gudumuwa yadda aka nema ba a lokacin da ake shirin kawo wannan kudiri.
Kungiyar ta Jama’atu Nasril Islam, tace a lokacin da aka nemi bangarorin addini su sa na su bakin wajen kawo wannan sabuwar doka da za ta yi wa addini garambawul, CAN ta zare jikin tane gaba daya.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
AREWASTARBLOG: Video: Kalli Yadda Ake Hada Connection Na Yadda Z... : Video: Kalli Yadda Ake Hada Connection Na Yadda Zaka Saurari Duk Kanin Kiran Da BUDURWARKA Takeyi Ko Akai Mata Ta Wayar Ka " SPY...
Comments