Skip to main content

MAN YAN HANYOYI 10 NA YIN ARZIKI

MANYAN HANYOYI GUDA GOMA-(10) NA SAMUN ARZIKI Arziqi yana da manyan hanyoyin samunsa guda biyu sune; *A-Hanyar samu🎆n Arziqi na Al'ada Wanda ya hada noma da kiyo da kasuwanci da kwadago*. *B-Hanyar samun arziqi na shari'a,sune wadan nan hanyoyi guda goma,wadanda suka tabbata daga Alqurani da Hadisan Manzon AllahSAW ingantattu* Dukkan Wanda yake neman Arziqi to wajibine ya bi daya ko wasu daga cikin wadan nan hanyoyi tare da doguwa ga Allah,sannan ya kuma yarda da abinda Allah ya bashi na kason arziqinsa. Daga Cikin ayoyin da suke bayani a akan arziqi da hanyar samun sun hada da;- ﻳﻘﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ;(ﻭَﻓِﻲ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀِ ﺭِﺯْﻗُﻜُﻢْ ﻭَﻣَﺎ ﺗُﻮﻋَﺪُﻭﻥَ‏) . *(Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari)*. @ﺳﻮﺭﺓ:ﺍﻟﺬﺍﺭﻳﺎﺕ. ﻭﻳﻘﻮﻝﺗﻌﺎﻟﻰ (ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻫُﻮَ ﺍﻟﺮَّﺯَّﺍﻕُ ﺫُﻭ ﺍﻟْﻘُﻮَّﺓِ ﺍﻟْﻤَﺘِﻴﻦُ ‏) . *(Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi)*. @ﺳﻮﺭﺓ : ﺍﻟﺬﺍﺭﻳﺎﺕ ﻭﻳﻘﻮﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ ‏(ﻫُﻮَ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺟَﻌَﻞَ ﻟَﻜُﻢُ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽَ ﺫَﻟُﻮﻟًﺎ ﻓَﺎﻣْﺸُﻮﺍ ﻓِﻲ ﻣَﻨَﺎﻛِﺒِﻬَﺎ ﻭَﻛُﻠُﻮﺍ ﻣِﻦ ﺭِّﺯْﻗِﻪِ ۖ ﻭَﺇِﻟَﻴْﻪِ ﺍﻟﻨُّﺸُﻮﺭُ). *(Shi, (Allah), Yã sanya muku ƙasa hõrarriya,sai ku tafi cikin sãsanninta,kuma ku ci daga arzikinSa,kuma zuwa gare shi ne tãshin yake)* @ﺳﻮﺭﺓ : ﺍﻟﻤﻠﻚ . HANYOYIN ARZIQI NA SHARI'A 1-HANYA TA FARKO *Yawaita Istighfari* Kaicon ga Wanda yake neman arziqi amma ya manta da hanya mafi sauki ta samun arziqi a wajen Allah,wato yawaita *ISTIGHFARI*. ALLAH YANA CEWA ‏(ﻓَﻘُﻠْﺖُ ﺍﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻭﺍ ﺭَﺑَّﻜُﻢْ ﺇِﻧَّﻪُ ﻛَﺎﻥَ ﻏَﻔَّﺎﺭًﺍ ‏( 10 ‏) ﻳُﺮْﺳِﻞِ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀَ ﻋَﻠَﻴْﻜُﻢْ ﻣِﺪْﺭَﺍﺭًﺍ( 11 ‏) ﻭَﻳُﻤْﺪِﺩْﻛُﻢْ ﺑِﺄَﻣْﻮَﺍﻝٍ ﻭَﺑَﻨِﻴﻦَ ﻭَﻳَﺠْﻌَﻞْ ﻟَﻜُﻢْ ﺟَﻨَّﺎﺕٍ ﻭَﻳَﺠْﻌَﻞْ ﻟَﻜُﻢْ ﺃَﻧْﻬَﺎﺭًﺍ ‏) . *(Shi na ce,'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku,lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne.""Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga.""Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna)*. @ﺳﻮﺭﺓ ﻧﻮﺡ ‏] Manzon Allah ﷺ yana cewa;- *(Dukkan Wanda ya lazumci yawaita ISTIGHFARI,to Allah zai Sanya masa mafita a duk lokacin da yake cikin qunci,kuma ya kawo masa farin ciki a duk lokacin da yake cikin damuwa,kuma ya azurta shi daga Inda baya tsammani)*. @ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ. 2-HANYA TA BIYU *Taqwa,wato jin tsoran Allah da kiyaye dokokin Allah,ta hanyar barin abinda yayi hani da aikata abinda yayi umarni* Allah yana cewa (وَيَرْزُقْهُ مِنْ حَيْثُ لَا يَحْتَسِبُ ۚ وَمَن يَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ فَهُوَ حَسْبُهُ ۚ إِنَّ اللَّهَ بَالِغُ أَمْرِهِ ۚ قَدْ جَعَلَ اللَّهُ لِكُلِّ شَيْءٍ قَدْرًا ) *(Kuma Ya arzũta shi daga inda bã ya zato.Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, Allah ne Ma'ishinsa. Lalle Allah Mai iyar da umurninSa ne.Haƙĩƙa Allah Ya sanyama'auni ga dukan kõme)* @ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻄﻼﻕ ‏ Kuma Allah yana cewa: ‏(ﻭَﻟَﻮْ ﺃَﻥَّ ﺃَﻫْﻞَ ﺍﻟْﻘُﺮَﻯٰ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﻭَﺍﺗَّﻘَﻮْﺍ ﻟَﻔَﺘَﺤْﻨَﺎ ﻋَﻠَﻴْﻬِﻢ ﺑَﺮَﻛَﺎﺕٍ ﻣِّﻦَ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀِ ﻭَﺍﻟْﺄَﺭْض‏) . @ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻷﻋﺮﺍﻑ Jin tsoron Allah hanya CE ta samun arzikin duniya dana lahira,jin tsoran Allah shine mabudin dukkan alkhairi,yawan sabon Allah itace makullin alkhairi kuma mabudin dukkan sharri. 3-HANYA TA UKKU *Dogaro ga Allah da sallamawa Allah ta hanyar yarda da samu da rashi daga Allah yake,tare da bin hanyoyin da Allah ya sanya na cin nasara da samun arziki sai kuma zuciyarka ta sallama tare da amincewa da yardar akan Allah kadai yake Qaddara samu ko rashi*. Allah yana cewa; ‏(وَيَرْزُقْهُ مِنْ حَيْثُ لَا يَحْتَسِبُ ۚ وَمَن يَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ فَهُوَ حَسْبُهُ ۚ إِنَّ اللَّهَ بَالِغُ أَمْرِهِ ۚ قَدْ جَعَلَ اللَّهُ لِكُلِّ شَيْءٍ قَدْرًا ) *(Kuma Ya arzũta shi daga inda bã ya zato. Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to,Allah ne Ma'ishinsa.Lalle Allah Mai iyar da umurninSa ne. Haƙĩƙa Allah Ya sanyama'auni ga dukan kõme)* @ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻄﻼﻕ ‏ Manzon Allah ﷺ yana cewa: *(Da dai zaku yi dogaro da Allah matuqar dogaro,da Allah ya azurta Ku kamar yadda yake azurta tsuntsu,zai wayi gari cikinsa babu komai,amma yayi yammaci cikinsa a cike)* @ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ Allah ne mafi sani Mu hadu A darasi na gaba insha Allah@.www.facebook.com/ibrahim sani hussain

Comments

Popular posts from this blog

Kungiyar IZALA tayi Allah wadai da cin Mutunci da yan kwankwasiyya suka yiwa Dr. Ali Pantami

Kungiyar IZALA tayi Allah wadai da cin Mutunci da yan kwankwasiyya suka yiwa Dr. Ali Pantami Daga Ibrahim Baba Suleiman Kungiyar wa'azin musulunci ta Izalatil Bid'ah wa Iqamatis Sunnah a Naijeriya, Tayi Allah wadai da cin Mutuncin da 'yan kungiyar kwankwasiyya sukayi wa ministan sadarwan Naijeriya Sheikh Dr. Isa Ali Pantami a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano dake Birnin kano. Shugaban IZALA Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau, shi yayi wannan kira ta wayar tarho daga Birnin Maiduguri jihar Borno a tarayyar Naijeriya, inda yake halartar wani taro a Birnin na Shehu. Sheikh Bala Lau yace, wannan al'amari akwai damuwa kwarai cikinsa, Malami mahaddacin Al'qur'ani, masanin tafsiri, Wanda ya kare rayuwarsa wajen aiki da fadakarwa akan addinin Musulunci, shine wasu 'yan Siyasa zasu masa irin wannan cin Mutunci tabbas an aikata laifi Babba. Shehin Malamin yayi kira da babbar murya cewa jagoran kwankwasiyya Dr. Rabi'u Musa kwankwaso ya fito ya baiwa ya...
DAKIN LABAREN  HAUSA 23 sep 2019 AURE KO ZAMAN GIDA? 1 - 2 AURE KO ZAMAN GIDA?    AURE KO ZAMAN GIDA? •••••••PART  1 ••••••••  HAUWA M.JABO akan hanyar asibiti nida qawata zeenah khalifa zamuje duba wata maqociyarmu da batada lafiya,Muna shiga asibiti mukayi karo da wata mata da yara guda biyu a hannunta zenah khalifa tayi sokoko tana kallonta.Ke zeenah khalifa kinji haushi ki kalli maza ki kalli mata.! Banason wulaqanci hauwa jabo.! Mikike nufi da inkalli mata in kalli maza? kamar wata bunsura..!!! Na kwashe dadariya nace yanzu dai yimin bayani mi kika hango.?? Ta kwashe da dariya kibari kawai,Hauwa jabo matar nan ta hadu billahillazi..Da ace ba baqa bace sai ince wllhy ba indiyace keni muje muyi qawance da ita,Ke zainab muna fama da talaucinmu za...