Skip to main content

WATA SABUWAR AMARYA

Wani mutum ne yayi sabuwar amarya, ba ta wuce kwanaki biyar(5) ba da auren su, sa angon ya tafi kasuwa domin yi mata cefane. Isowar shi gida keda wuya sai yaga wata babbar mota a kofar gidan sa kai da ganin motar kasan cewa wanda yake hawanta matashin me kudi. Da shigar shi gida saiya nufi dakin Amarya har izuwa uwar daka, yana isowa saiya yayi kacibus da wani mutum kwance a kan gadon amarya yana ta sharar barci abinsa, Sai ya tafi kitchen ya tambayi Amarya? Wane ne a dakin ki,? Budan bakin ta sai tace: Ohhhhhh Amir ne muna kiran shi(Aji dadi) a WhatsApp. Related Posts Yanzu ma haka shi nake soyawa kajin daka siyo kace a soyawa su ummah idan sun zo. Amir ya sha tafiya ya gaji(WALLAHI) abokina ne A WhatsApp muka hadu, kwanakin baya ma da nayi tafiya na kashe waya ta ai abuja nakai mishi Ziyara, kwana bakwai nayi, Sharaton hotel ya kam min. Yanzu ma haka shi ba dadewa zaiyi ba, bai wuce yayi kwana uku(3) ba don haka kawai na yanke shawara akan ya zauna a daki na kafin ranar tafiyar sa. Ga mukullin motar sa yaba ni ya ce idan ka dawo ka shigo mai da ita saboda bai kamata ya shigo da mota ba tare da izinin mai gida ba!!!!.

Comments

elbasawee.com said…
To allah shikyauta

Popular posts from this blog

Kungiyar IZALA tayi Allah wadai da cin Mutunci da yan kwankwasiyya suka yiwa Dr. Ali Pantami

Kungiyar IZALA tayi Allah wadai da cin Mutunci da yan kwankwasiyya suka yiwa Dr. Ali Pantami Daga Ibrahim Baba Suleiman Kungiyar wa'azin musulunci ta Izalatil Bid'ah wa Iqamatis Sunnah a Naijeriya, Tayi Allah wadai da cin Mutuncin da 'yan kungiyar kwankwasiyya sukayi wa ministan sadarwan Naijeriya Sheikh Dr. Isa Ali Pantami a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano dake Birnin kano. Shugaban IZALA Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau, shi yayi wannan kira ta wayar tarho daga Birnin Maiduguri jihar Borno a tarayyar Naijeriya, inda yake halartar wani taro a Birnin na Shehu. Sheikh Bala Lau yace, wannan al'amari akwai damuwa kwarai cikinsa, Malami mahaddacin Al'qur'ani, masanin tafsiri, Wanda ya kare rayuwarsa wajen aiki da fadakarwa akan addinin Musulunci, shine wasu 'yan Siyasa zasu masa irin wannan cin Mutunci tabbas an aikata laifi Babba. Shehin Malamin yayi kira da babbar murya cewa jagoran kwankwasiyya Dr. Rabi'u Musa kwankwaso ya fito ya baiwa ya...
DAKIN LABAREN  HAUSA 23 sep 2019 AURE KO ZAMAN GIDA? 1 - 2 AURE KO ZAMAN GIDA?    AURE KO ZAMAN GIDA? •••••••PART  1 ••••••••  HAUWA M.JABO akan hanyar asibiti nida qawata zeenah khalifa zamuje duba wata maqociyarmu da batada lafiya,Muna shiga asibiti mukayi karo da wata mata da yara guda biyu a hannunta zenah khalifa tayi sokoko tana kallonta.Ke zeenah khalifa kinji haushi ki kalli maza ki kalli mata.! Banason wulaqanci hauwa jabo.! Mikike nufi da inkalli mata in kalli maza? kamar wata bunsura..!!! Na kwashe dadariya nace yanzu dai yimin bayani mi kika hango.?? Ta kwashe da dariya kibari kawai,Hauwa jabo matar nan ta hadu billahillazi..Da ace ba baqa bace sai ince wllhy ba indiyace keni muje muyi qawance da ita,Ke zainab muna fama da talaucinmu za...