Yanzu Yanzu: Boko Haram sun karbe wani gari a Borno
Updated: 2 hours ago
Author: Abubakar Nura Bala
Views: 1350
Category: Labarai
FACEBOOK EMAIL
TWITTER WHATSAPP
FACEBOOK MESSENGER TELEGRAM
Rahotanni da ke zuwa mana daga jaridar Daily Trust ya nuna cewa a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni yan Boko Haram sun amshe garin Marte, hedkwatar karamar hukumar Marte dake jihar Borno.
Daya daga cikin majiyan da suka tabbatar da lamarin, yace yan ta’addan sun shigo sansanin rundunar sojin bataliya na 133, inda suke ta harbe-harbe ba kakkautawa sannan a sanadiyar haka suka kacalcala komai.
“Da alama yan ta’addan basu zo da niyyar illata yan farar hula ba, sun zo ne da niyyan amshe garin, wannan yasa suka shiga sansanin sojojin ba tare da sanarwa ba da misalin karfe 6pm, kimanin kasa da awa daya kafin lokacin bude baki,” majiyar ta tabbatar.
Wani majiyi ya kuma bayyana cewa sun yi arangama da yan ta’addan inda saur kiris su yi gababa a kansu.
Ya kara da cewa “Ina iya fada muku cewa muna dab da cin galaba akansu; amman Allah ne masanin dabaru da suka yi amfani da shi, wanda hakan yasa suka yi nasara a kanmu; a halin yanzu garin ya koma karkashin kulawansu.”
A cewar wani majiyin da ya tsere, “baza a iya tabbatar da adadin wadanda suka ji rauni ba a bangaren biyu bayan duk mun tsere cikin daji guda, inda yawancinmu suka nemi hanya zuwa Maiduguri sannan har yanzu yawanci suna cikin jeji suna neman mafita."

Comments