Shugaba Buhari zai daga zuwa kasar Liberia don halartar taro da kuma karbar wata muhimmiyar kyauta a kasar
Written by Ibrahim sani hussain 17 minutes ago - Shugaban kasa Buhari zai daga zuwa kasar Liberia a ranar Juma'a, 25 ga watan Yuli - Buhari zai halarci taron taron bikin samun 'yancin kan kasar sannan zai karbi lambar yabo na musamman a kasar - Daga cikin wadanda za su masa rakiya akwai gwamnoni uku, sakataren dindindin na ma'aikatar harkokin waje da wasu manyan jami'an gwamnati Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli zuwa Monrovia, kasar Liberia domin halartan bikin zagayowar raanar yancin kan kasar karo na 172. Bayan kasancewarsa babban bako na musamman a wajen taron, za a karrama Shugaban kasar da karramawa mafi daraja a kasar. A wani jawabi daga babban hadimin Shugaban kasar a kafofin watsa labarai, Garba Shehu, ya kuma bayyana cewa gwamnatin kasar ce za ta gabatar da lambar yabon ga Buhari akan kokarinsa kan lamuran kasashen duniya, gwamnati, addini, da dai sauransu. Shugaban kasar zai samu rakiyar wasu gwamnoni da suka hada da Kayode ayemi, Abdulrahman Abdulrazaq da kuma Mai Mala Buni. Sauran masu rakiyan sun hada da sakataren dindindi na ma’aikatar harkokin waje, Ambasada Mustapha Sulaiman da sauaran manyan jami’an gwamnati.
Comments