Kenya: Aji ya rushe ya kashe yara bakwai a makaranta
2 Satumba 2019
Dalibai hamsin da bakwai ne ke karbar magani a asibiti sakamakon rushewar da ajinsu ya yi a wata makaranta da ke Nairobi, babban birnin kasar Kenya.
A kalla yara bakwai ne suka mutu lokacin da rufin katako na makarantar Precious Talent School ya fado wa yaran da ke karatu a ajin da ke ginin kasan benen ranar Litinin.
Rahotanni sun ce gomman yara ne suka makale a cikin ajin. Tuni jami'an agaji suka isa wajen da lamarin ya faru
Masu aikin ceto sun sha wahala kafin su kutsa kai cikin makarantar saboda cincirindon jama'a da suka taru a wajen.
Kungiyar Red Cross ta kasar ta bayyana cewa ta bude cibiyar samun bayanai a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, domin taimaka wa iyayen da 'ya'yansu suka bata a hatsarin.
Iyayen da 'ya'yansu suka samu raunuka sun garzaya babban asibitin kasar na Kenyatta National Hospital inda suke sauraron halin da 'ya'yansu ke ciki.
Dalibai da yawa dai sun gudu zuwa wata unguwar Dagoretti dake yammacin birnin, bayan da ginin ya ruso, a cewar manajan makarantar Moses Wainaina Ndiragu.
Comments