Skip to main content

ABUBUWAN DA SUKE WARWARE MUSULUMCI

ABUBUWAN DA SUKE WARWARE MUSULUMCI
            •┈┈•⊰✿✿⊱•┈┈•

Shaikh Muhammad Bin Abdilwahhab Allah ya yi masa rahama ya ce:

Ka sani lallai mafi girman abubuwan da suke warware musulunci guda goma ne

1-SHIRKA a cikin bautar Allah Madaukakin Sarki; dalili a kan haka fad'in Allah Madaukakin Sarki:

"إِنَّ اللَّهَ لَا يَغْفِرُ أَن يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَاءُ".

"Lallai ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki game da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake bãyan wannan ga wanda Yake so.."[An-Nisaa:48]

Kuma yana  daga  cikin  Shirka:  yin yanka domin  wanin  Allah,  kamar  wanda  zai yi yanka domin aljani ko kuma domin k'abari.

2-Duk wanda ya sanya tsani a tsakaninsa da Allah, yana kiran wannan tsanin yana rokonsu yana kuma dogara a kansu, ya kafirta babu wani sabani.

3-Duk wanda bai kafirta mushrikai ba, ko kuma ya yi shakkan kafircinsu, ko ya inganta ra’ayinsu, to ya kafirta.

4-Wanda  ya  kudurta cewa lallai sabanin  karantarwar  Annabi SAW shi ne mafi cika a kan shiriyarsa, ko kuma hukunce-hukuncen waninsa su ne mafi kyawu a kan hukunce-hukuncensa, kamar dai wanda ya ke fifita hukunce-hukuncen dagutai a kan hukunce-hukuncensa.

5-Wanda duk yayi fishi da wani abu cikin abin da Annabi SAW ya zo da shi, ko da kuwa ya yi aiki da shi to ya kafirta. Dalili a kan haka fad'in Allah Madaukaki:

"ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ كَرِهُوا مَا أَنزَلَ اللَّهُ فَأَحْبَطَ أَعْمَالَهُمْ"

"Wannan, sabõda lalle sũ, sun ƙi abin da Allah Ya saukar dõmin haka Ya ɓata ayyukansu." [Muhammad:9]

6-Wanda ya yi izgili da wani abu na Addinin, ko (izgili da) ladan da Allah zai bayar (a kan wani aiki) ko ukubar da Allah ya tanada, to ya kafirta, dalili a kan haka fad'in Allah Madaukakin Sarki:

"قُلْ أَبِاللَّهِ وَآيَاتِهِ وَرَسُولِهِ كُنتُمْ تَسْتَهْزِئُونَ".

"Ka ce: "Shin da Allah, da kuma ãyõyinSa da ManzonSa kuka kasance kunã izgili?"[At-Tawba:65].

"لَا تَعْتَذِرُوا قَدْ كَفَرْتُم بَعْدَ إِيمَانِكُمْ".

"Kada ku kãwo wani uzuri, haƙĩƙa, kun kãfirta a bãyan ĩmãninku."[At-Tawba:66].

7-Asiri(Sihiri), kuma yana daga cikin nau’ikan sihiri: "Kautarwa’" da "Kimsawa" wato a kautar da mutum daga abin da yake so yake bukata, ko kimsa masa abin da bai so a sa mishi son sa, wanda duk ya aikata wannan ko kuma ya yarda da shi to ya kafirta, dalili a kan haka fad'in Allah Madaukaki:

"وَمَا يُعَلِّمَانِ مِنْ أَحَدٍ حَتَّىٰ يَقُولَا إِنَّمَا نَحْنُ فِتْنَةٌ فَلَا تَكْفُرْ"

 "Kuma ba su sanar da kõwa ba balle su ce: "Mũ fitina kawai ne, sabõda haka kada ka kãfirta," [Al-Baqara:102].

8-Taimakon mushrikai da agaza musu a kan musulmai, dalili a kan haka fad'in Allah Madaukaki:

"وَمَن يَتَوَلَّهُم مِّنكُمْ فَإِنَّهُ مِنْهُمْ ۗ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ."

"Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, lalle ne shĩ, yanã daga gare su. Lalle Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai. [Al-Maa'ida:51]

9-Wanda duk ya kudurce cewa; lallai wasu cikin mutane ba ya wajaba a kansu su bi Manzon Allah SAW, Kuma cewa yana yiwuwa ga wasu daga cikin mutane su fita daga shari’arshi(SAW), kamar  yanda  ya  yiwu  ga  Khidr fita  daga  Shari’ar Annabi Musa(AS),to shi kafiri ne.

10-Kawar da kai daga Addinin Allah Madaukaki, ba ya koyonshi kuma ba ya  aiki  da  abin da Addinin  ya  koyar,  dalili a kan haka fad'in Allah Madaukakin Sarki:

"وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّن ذُكِّرَ بِآيَاتِ رَبِّهِ ثُمَّ أَعْرَضَ عَنْهَا ۚ إِنَّا مِنَ الْمُجْرِمِينَ مُنتَقِمُونَ".

"Kuma wãne ne ya fi zãlunci bisa ga wanda a ka tunãtar da ãyõyin Ubangijinsa, sa'an na ya bijire daga barinsu? Lalle Mũ, Mãsu yin azãbar rãmuwa ne ga mãsu laifi.[As-Sajda:22]

Kuma babu bambanci a kan dukka  wadannan abubuwa masu warware Tauhidi tsakanin wanda ya yi su da wasa  da  kuma  wanda  ya ke  da  gaske,  da  kuma  mai  tsoro  sai dai  kawai  wanda  a ka tilasta masa.

Kuma duka wadannan suna da matukar hadari, kuma suna cikin abin da ya ke yawan aukawa, don haka ya kamata ga dukkanin musulmi ya kiyayesu kuma ya ji tsoronsu a kansa.

Muna neman tsarin Allah, ya tsaremu daga abubuwan da suke haifar da fushinSa, da kuma zazzafar ukubarSa.

Tsira  da  amincin  Allah  su  tabbata  ga   Annabinmu  Muhammad,  da Iyalansa da kuma Sahabbanshi.

نواقض الإسلام لإمام الدعوة الشيخ محمد بن عبد الوهاب بن سليمان التميمي.

#Zaurandalibanilimi

https://t.me/Zaurandalibanilimi

https://www.facebook.com/Zaurandalibanilimi/
  09/02/2019
•┈┈•⊰✿✿⊱•┈┈•

Comments

Popular posts from this blog

A MAN WAS CRYING

A man was crying😭 and someone asked him why he was crying. And he said I have only one son, I have done all my possible best to educate him so that he will be a great person and by Allah's grace he has been able to acquire all certificates including: 🌺 J.S.C.E. 🌺 S.S.C.E. 🌺 Bachelor's Degree. 🌺 MSc. 🌺 Phd. BUT! Unfortunately, he fell sick and doctors said they can't do anything about his condition and the only option is to die in the next 30 minutes and my son told me to bring all his certificates and I brought them. All he could say was; father, these are my degrees but you never told me to study my Qur'an. I don't know what I'm going to tell Allah! Most of us will not share this message because it is not an interesting joke. But if you are willing enough to share this message, please do so and Allah will never forget what you have done. PLEASE LET US TAKE NOTE OF THESE: 🌹Study the Qur'an like the way you study your notes when it is exams

Labarin 'yan shi'a

Labari da dumi duminsa    'Yan Shi'a sun dakatar da zanga-zanga, sun bayyana dalilansu Kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) ta aka fi sani da Shi'a ta sanar da cewa za ta dakatar da zanga-zangar da ta keyi na dan wani lokaci. Shugaban fanin yada labarai na kungiyar ta IMN, Ibrahim Musa ne ya sanar da hakan cikin wata jawabi da ya fitar a ranar Laraba. Gwamnatin Tarayya ta ayyana kungiyar a matsayin na ta'addanci tare da haramta ayyukan kungiyar bayan kotun tarayya da ke Abuja ya ayyana kungiyar a matsayin na ta'addanci. Musa ya ce an dauki matakin dakatar da zanga-zangar ne sakamakon 'wasu sabbin hanyoyi da suke bude na warware matsalar' da ke da alaka da haramta ayyukan kungiyar. Ya ce kungiyar ta dauki matakin dakatar da zanga-zangar ne saboda girmama wasu manyan mutane da suka saka baki kan batun . Ya kara da cewa idan har aka samu wasu suna zanga-zanga a wani sashi na kasar, hakan ka iya faruwa ne idan wasu ba su fahimci sakonsa ba ko kuma sharri

TIRKASHI- WATA SABUWA INJI 'YAN CHA-CHA

Za a kasa kudaden marigayi Abacha tsakanin kasashe uku Najeriya da Amurka da tsibirin Jersey sun ce za su kasafta fiye da dala milyan 267 da tsibirin Jersey ya kwace daga irin kudaden da ake zargin gwamnatin tsohon shugaban Najeriya na soja, marigayi janar Sani Abacha ta sata ta jibge a bankunan kasar. A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai aka sanya dala 267 a cikin wani asusu na musamman da gwamnatin kasar ta Jersey ta kafa domin zuba irin wadannan kudade masu kama da ganima. Wani wakili daga ofishin ministan shari'ar kasar ya shaida wa BBC cewa har kawo yanzu Jersey ba ta kammala tantance hanyar da za ta bi ba wajen kasafta kudaden ba. Sai dai ya ce gwamnatin tsibirin za ta zauna da Najeriya da Amurka domin tattauna yadda za su raba kudin a tsakaninsu. Gwamnatin Najeriya za ta rabawa talakawa kudaden Abacha 'Kudin da Abacha ya sace': Switzerland za ta mayar wa Nigeria $320m A baya dai wata kotu a Amurka ta gano kudaden wadanda ta ce an fitar da su daga Najeriya ta wasu