DAKIN LABAREN HAUSA 23 sep 2019 KARKEN ALEWA KASA, BATURE GAGARE Page 1 Episode 1 KARKEN ALEWA KASA, BATURE GAGARE Daga littafin Karshen Alewa Kasa Na Bature Gagare (c) NNPC Nigeria BABI NA FARKO TSAUNIN GWANO Tin kwal, Tin kwal, kwal! Tin kwal, Tin kwal Kwal… Mai yin shela ya bar kada kugensa domin ya yi jawabi a wani dan lungu da ya shigo. Ya kafa hannu a baki yayi kira, “Hyai, hyai, ina mazajen Tsaunin Gwano, sarkin kira ya gaishe ku. Bayan gaisuwa ya ce a fada muku lokaci ya yi wanda duk mai ji da kanshi ya shirya…” Ya wuce gaba yana kada kuge yana fadar sako rariya rariya. Hantsi ya ajiye kokon da ya gama shan burkutu da shi, ya yi wata doguwar mika ya yi murmushi, “To fa mutane, ga Audun makeri can yana buga kugen tasa. Yaya ka ji Mailoma?” Wani saurayi da ake kira Mailoma yana zaune a kan wani buzu da aka yi da fatar biri ya miko hannu suka tafa, ”Haba Hantsi,” in ji shi, “Ai ni nan wurin duk sun tsima ni kuma, sai na ji ma giyar nan duk ta fita raina.” Sai wuf ya mike tsaye ...